Anyi itifakin cewar rashin aikinyi yafi Kamari a jahar Kano a cewar hukumar samar da guraben aikin yi. Shi kuma shugaban shirye shirye na hukumar kyautata da’a ta jahar Kano Dr. Kabiru Musa Shu’aibu yace gwamnatin jahar Kano ta samar da guraben ayyuka ga matasa.
Yace duk matasa da suka halaci makarantun kimiya da fasaha, yanzu akwai damar daukansu aiki a ma’aikatar lafia, don yanzu haka gwamnati ta kirkiro da wani shiri da a ke kira Lafia Jari, kuma shi wannan shirin don a taimaka ma marasa aikin yi ne da kuma taimakama al’umma.
Kana kuma ta bangaren Mahauta gwamnati tasa anzabo mutane dubu goma wanda akabasu horo, wanda bayannan an basu jari wanda zai taimakamusu don su gyara sama’arsu da tsafta. Abu mai matukar mahimmanci shine gwamnati ta hana yawon bara, don haka kuma za’a samamusu sana’a da tayi daidai da su.