Rasha Ta Tura Kayan Yaki Syria Ta Taimakawa Gwamnatin Kasar

John Kerry, Sakataren Harkokin Wajen Amurka

Sakataren harkokin wajen Amurka yace Rasha ta tura kayan yaki Syria ne domin ta taimakawa gwamnatin kasar

Sakataren Harkokin Wajen Amurka John kerry, yace sojin Amurka da suka kware ta fuskar tsaro sun hakikance cewa Rasha ta tura jiragen yaki da wasu karikitanta ne zuwa sham ko Syriadomin kare dakarunta da tuni tura cikin kasar.

Duk da haka sakatare Kerry ya fada jiya Talata cewa, har yanzu ba'a tantance burin Rasha a Syria ko na lokaci mai tsawo ne ba. Yace idan Rasha tana haka ne domin ta bunkasa martabarta a yankin Gabas ta tsakiya, to ta fara sakar da bakin zare, domin tana goyon bayan gwamnatin Syria wacce take aikata ba dai dai ba.

Rasha dai tace tana so ta taimaka wajen yaki da 'yan kungiyar ISIS, amma taki ta shiga runduar taron dangi da Amurka take yiwa jagoranci wajen yaki da masu tsatsaurar raayin addinin Islama ba.

Daga nan Mr. Kerry ya bayyana fatar cewa kasashen Rasha da Iran da wasu kawayen Syria, sun shirya domin ganin an sami zaman lafiya a Syria.