Rashin Katin Shadar Zama Dan Kasa Ya Sa Al'ummar Borno da Yobe Kokawa

Sojojin Najeriya

Tun da aka fara aikin bada katin shadar zama dan kasa ba'a taba bude ofisoshin masu bada katin ba a jihohin biyu.

Rashin bude ofisoshin a Borno da Yobe yana da nasaba da rashin tsaro a jihohin biyu.

Fiye da shekara daya ke nan da gwamnatin tarayya ta soma bada katin shaidar zama dan kasa na din-din-din amma tashe-tashen hankula sun hana jihohin biyu jin duriyar katin.

Yanazu al'ummar jihohin suna kokawa kan rashin samun katin musamman idan an yi la'akari da cin zarafin da jami'an tsaro ke yi masu saboda rashin katin.

A jihohin duk wanda bashi da kati jami'an tsaro na ji masa . Idan sun tare mutum sai sun tatseshi da tara da kan kama tsakanin nera 600 zuwa 1000.

Ofisoshin masu bada katin yanzu babu kowa cikinsu. An dauke ma'aikatan an turasu wasu jihohin.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Rashin Katin Shaidar Zama Dan Kasa Ya Sa Al'ummar Borno da Yobe Kokawa - 3' 07"