Rayuka 26 Sun Salwanta a Harin Da Boko Haram Ta Kai Adamawa

Wani sansanin 'yan kungiyar Boko Haram da dakarun Najeriya suka daidaita a arewa maso gabashin Najeriya

Rahotanni daga Najeriya na cewa, mayakan Boko Haram sun kai hari a wani kauyen jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya, inda suka halaka mutum 26.

Wadanda suka shaida harin sun tabbatar Muryar Amurka cewa, mayakan na Boko Haram sun kai farmaki ne a garin Kuda Kaya da ke da tazarar kilomita shida da shedikwatar karamar hukumar Madagali inda aka samu asarar rayuka sama da 20.

“Mutum kusan 30 aka kashe, kuma babu gida ko daya da ya rage a wannan kauye” a cewar wani mazaunin yankin da ya sulale ya bar garin.

Da yake karin haske, wani tsohon shugaban karamar hukumar ta Madagali, Abawu Maina Ularamu, ya ce yanzu haka suna cikin halin zaman dar dar sakamakon irin hare haren da ake kai musu cikin kwanakin nan.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ta Adamawa, DSP Othman Abubakar, ya tabbatar da aukuwar wannan lamarin da kuma irin matakin da aka dauka inda ya bukaci jama’a da su rika ba su bayanai a duk lokacin da ba su amince da wani ko wasu ba.

Rayuka da dama ne dai suka salwanta ta sanadiyar hare-haren Boko Haram da aka shafe fiye da shekaru bakwai ana fama da su.

Saurari cikakken rahoton Ibrahim Abdulaziz daga Yola:

Your browser doesn’t support HTML5

Rayuka 26 Sun Salwanta a Harin Da Boko Haram Ta Kai Adamawa - 2'10"