Real Madrid Na JIran A Hura Tashi Ne Kawai A Wasanta Na Yau Da Borussia Dortmund - 8/4/2014

Cristiano Ronaldo

Real Madrid da Borussia Dortmund yau talata a karawa ta biyu ta wasan kwata fainal a gasar cin kofin zakarun kulob na Turai.

A wannan wasan, ‘yan kallon tamaula sun ce su na jira ne kawai su ji an hura tashi, Real ta yi nasara, ganin yadda ta kanainaye kwallo a karawar farko, ta jefa uku a raga. Ita kuwa Dortmund ta kasa tabuka komai.

A yau, tana bukatar ta jefa kwallaye har 4 da babu kafin ta wuce, abinda zai yi wuya. Idan har Real Madrid ta jefa ko da kwallo guda ne, to dole sai Dortmund ta jefa kwallaye har biyar kafin ta iya hayewa. Wannan ba karamin aiki ba ne.

Wadanda suka lashe wasannin na yau, zasu haye zuwa wasan kusa da karshe, inda zasu jira wadanda zasu yi nasara a wasannin gobe: Manchester United da Bayern Munich da kuma Atletico Madrid da FC Barcelona.