WASHINGTON, DC —
Hausawa suka ce karshen tika-tika, Tik! Jiya dai an doke kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich, a karon farko cikin wasanni 53 a Bundesliga, watau gasar lig-lig ta Jamus. Kungiyar Augsburg, ita ce ta doke Bayern da ci 1-0. Har ila yau, wannan shi ne karon farko da aka hana ‘yan Bayern jefa kwallo cikin raga a wasanni 65. Rabon da ba a ce Bayern ta jefa kwallo a raga ba tun wasanta da Mainz a ranar 14 ga watan Afrilun shekarar 2012.
Sai dai manajan Bayern, Pep Guardiola, yace babu damuwa, tunda su a wurinsu, wasan Bundesliga ya riga ya kare, sun riga sun lashe. Yanzu zasu mayarda hankalinsu a kan gasar zkarun kulob kulob na Turai ne.
A Ingila, Chelsea ta doke Stoke City da ci 3-0, ta koma saman teburin Firimiya na Ingila, akalla na wani dan lokaci. Liverpool da Manchester City, su na ci gaba da auna wannan kujerar.
A Spain ma dai abin haka yake, inda har yanzu maki daya ya raba tsakanin Atletico madrid da FC Barcelona. Dukkan kungiyoyin biyu sun samu nasara jiya, suka ci gaba da zaman diris a kan inda suke, a bayan da Atletico ta doke Villareal da ci 1-0, ita kuma FCB ta doke Real Betis da ci 3-1.