Real Madrid Tana Ba Bayern Munich Kashi - 29/4/2014

Cristiano Ronaldo, hagu, yana taya Sergio Ramos murnar jefa kwallon farko yau talata a ragar 'yan Bayern Munich. ya zuwa yanzu dai Ramos ya jefa kwallaye biyu.

Sergio Ramos ya narka kwallaye biyu a ragar 'yan Bayern Munich a karawa ta biyu da kungiyoyin biyu keyi domin fitar da wadda zata je ga wasan karshe na cin kofin zakarun kulob na Turai.

A karawar farko, Real Madrid ce ta yi nasara da ci 1 da babu. Yanzu dai ana 3 da babu ke nan, kuma Bayern Munich zata bukaci kwallaye 4 idan Real ba ta kara ko guda ba, domin ta samu hayewa.

Real Madrid ta kara jefa kwallo na uku, yanzu ana 3-0. ma'ana dai Bayern tana bukatar kwallaye biyar kafin ta haye zuwa wasan karshe.

Cristiano Ronaldo da Sergio Ramos