Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Za A Fitar Da Gwani A Tsakanin Real Madrid Da Bayern Munich - 29/4/2014

Arjen Robben da Frank Ribbery na Bayern Munich su na daga hannu a kusa da Daniel Carvajal na Real Madrid a karawarsu ta farko makon jiya
Arjen Robben da Frank Ribbery na Bayern Munich su na daga hannu a kusa da Daniel Carvajal na Real Madrid a karawarsu ta farko makon jiya
Nan zuwa daren yau talata, za a san ko wacece a tsakanin Real Madrid da Bayern Munich zata kai labari zuwa ga wasan karshe na cin kofin zakarun kulob-kulob na Turai. Yanzu haka ‘yan Real Madrid su na can birnin Munich, domin kare ci daya da babun da suka yi ma zakarun na Jamus a karawarsu ta farko a makon jiya.

Wani abin murna ga ‘yan Real Madrid shi ne cewa da alamun ciwon da zakaransa Cristiano Ronaldo ya ji a kafa ya warke, domin a karshen mako, ya buga wasan minti 60, har ya jefa kwallaye biyu a wasan lig da suka buga da Osasuna.

Idan har Real ta jefa koda kwallo guda ne a raga a wasan yau, to fa tilas sai Bayern ta jefa kwallaye har uku kafin ta iya shigewa. Masana tamaula su na hasashen cewa zai yi wuya Bayern, wadda a baya-bayan na ta fara yin tuntube, ta jefa kwallaye har uku a ragar Real Madrid.

Za a fara wannan wasa da karfe 7:45 na daren yau talata agogon najeriya.

A gobe dai za a buga wasa na biyu a tsakanin Chelsea da daya kungiyar ta Madrid, Atletico. Za a buga wasan karshe na cin kofin zakarun kulob na Turai na bana a birnin Lisbon ta kasar Portugal a ranar 24 ga watan Mayu.
XS
SM
MD
LG