Rikici Tsakanin Makiyaya da Manoma a Nijar Ya Hallaka Mutane Shida

Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar

Kimanin mutane shida aka kashe a wasu garuruwan Jamhuriyar Nijar sanadiyar barkewar fada tsakanin makiyaya da manoman yankunan arewacin jihar Maradi.

Da zara damina ta kama fada kan barke tsakanin manoma da makiyaya. Tsalar shan ruwan dabbobi da cin gonaki ke haddasa rikicin.

Malam Yunusa Alatarafat wani ganao da rikicin ya taba a kokarin da ya yi na raba fadan ya ji rauni har ma sai da aka kaishi asibitin birnin Maradi.

Yace yana dawowa daga gona sai aka ce ana rikici wajen wani tafki. Yace sai suka shiga bada hakuri kowa ya kai zuciya nesa tunda an kira jandarmomi, wato 'yansanda ke nan. To amma yawancinsu basu da hakuri.

Malam Yunusa ya ce taimako ya je yi domin ya raba fada amma sai abun ya rutsa dashi. Yace an bugeshi a kugu da hannu da wasu wurare a jikinsa.

Bugu da kari rikicin ya raunata mutane tara da yanzu suna karbar magani a asibitin dake Maradi. Malam Abdulrahaman Zeidi mai kula da harkokin asibitin ya kara bayani. Cikin mutanen farko uku da aka kai asibitin daya ya riga ya mutu amma biyun an yi masu aikin tiyata na gaggawa. Daga baya kuma an kawo mutane shida tare da gawa daya.

Kawo yanzu dai mahukunta sun tsaurara matakan tsaro domin tabbatar da zaman lafiya.

Ga rahoton Shuaibu Mani da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Fadan Manoma da Makiyaya a Jamhuriyar Nijar Ya Hallaka Mutane Shida