Rikicin Siriya Ya Tilastawa 'Yan Kasar Miliyan Hudu Arcewa

Hukumar lura da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya yau Alhamis tace Syriyawa miliyan 4 ne suka arce daga kasarsu saboda rigingimu kuma yanzu sun zama ‘yan gudun hijira.

Bayanan wannan hukumar da aka fi sani da UNHCR a takaice sun nuna cewa akwai karin ‘yan gudun hijira miliyan 1 a watanni 10 da suka gabata, da kuma mutane miliyan 2 da dubu dari 4 a shekaru biyu da suka gabata, a dai-dai wannan lokaci da rigingimun na Syriya suka gagara nuna alamun sassautawa.

Abunda ya samo asali a watan Maris na 2011 daga zanga-zangar lumana dake adawa da gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad, shine ya tabarbare ya koma yakin basasar da yanzu ya hada da kungiyoyin ‘yan tawaye, da ma mayakan IS dukkaninsu suna fada juna da kuma rundunonin sojiji dake goyon bayan gwamnatin Syria.

Duk da kiraye-kirayen kasa da kasa na gani an kawo karshen wannan bata-kashi, da kuma zama akan teburin shawarwari har sau biyu a shekarar da ta gabata, har yanzu ana cigaba da tashe-tashen hankula dake lakume rayukan Syriyawa da kuma tursasawa jama’a tserewa daga gidajensu.