Rikicin Siyasa A Jamhuriyar Nijar

Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar

Da alamu akwai rarabuwar kawuna a jam'iyyar adawar Jamhuriyar Nijar dangane da shiga gwamnati
Akwai rashin jittuwa cikin jama'iyyar adawar Jamhuriyar Nijar dangane da shiga gwamnatin kasar.

A yayin wani taron kolin jam'iyyar adawa MNSD Nasara ta yi jiya ta yanke shawarar kin shiga gwamnatin kasar sabanin shawarar da ta tsayar a taronta na watan da ya wuce na shiga gwamnati kamar yadda shugaban kasar ya bukaceta ta yi. Wani dan majalisar kasar wanda yaki cikin jam'iyyar adawa yace kin shiga gwamnatin ya biyo bayan kasawar gwamnati wurin cika wasu ka'idoji da jam'iyyarsa ta tsara ma gwamnatin. Jam'iyar ta ce bata gamsu da sharrudan da gwamnati ta yi ba don haka ba zata shiga gwamnati ba.

Sai dai a wani lamari da ya yi kama da rudani wasu 'yan majalisu bakwai daga jam'iyyar sun amince da shiga gwamnatin duk da hukuncin kin yin hakan da uwar jam'iyyarsu ta yanke. Dan majalisa Yau Mohammed ya ce sun baiwa gwamnati sharruda uku kuma gwamnati ta cikasu don haka shi da sauran 'yan majalisu shida basu ga dalilin da ba zasu shiga gwamnatin ba. Ya ce su talakawa suka zabesu. Talakawa suke yiwa aiki. Shigansu gwamnati zai kawo ma kasarsu cigaba.

Yunkurin kawo 'yan adawa cikin gwamnati yana cigaba da jawo cecekuce a kasar har ma a tsakanin jam'iyyun kawance dake cikin gwamnatin wadanda suka ce shawarar kawo 'yan adawa cikin gwamnati ba'a yi da su ba. A cewarsu da can idan matsala ta taso ana zama dasu, wato su da suke cikin kawancen gwamnati a nemi shawararasu. Don haka basu san yadda za'a gayyato jam'iyyar adawa cikin gwamnati ba.

Yanzu dai 'yan Nijar sun sa ido su ga yadda za'a kare.

Ga rahoton Abdullahi Maman Ahmadu.

Your browser doesn’t support HTML5

Rikicin Siyasa A Jamhuriyar Nijar-3.10