Ronaldo Ya Kamu Da Cutar COVID-19

  • Murtala Sanyinna

Dan wasan kwallon kafa Cristiano Ronaldo.

Sahararren dan wasan kasar Portugal da ke taka leda a kungiyar Juventus ta kasar Italiya Cristiano Ronaldo ya kamu da cutar coronavirus.

Ronaldo ya nuna alamun rashin lafiyar ne, inda daga bisani aka auna shi, aka kuma tabbatar ya kamu da cutar ta COVID-19. Tuni dai da aka killace dan wasan.

Cristiano Ronaldo

Hukumar kwallon kasar Portugal ta ba da sanarwa kwanaki biyu bayan da kasar ta yi kunnen doki da Faransa ba wanda ya zura kwallo, cewa Ronaldo ba zai sami buga wasan gasar League ta kasashe ba da Portugal din za ta buga da Sweden a ranar Laraba a Lisbon.

To sai dai ta ce an auna sauran ‘yan wasan kasar a jiya Talata amma duk ba su kamu da cutar ba, don haka za su ci gaba da atisaye da yammacin ranar.

An dage atisayen ne da aka shirya gudanarwa da safe, to amma hukumar kwallon kasar bata bayar da dalilin dagewar ba.

Kafin tafiyarsu kasar Faransa, an auna dukkan ‘yan wasan Portugal din inda aka sami ‘yan wasa biyu dauke da cutar da suka hada da mai tsaron gida Anthony Lopes da ke taka leda a kungiyar Lyon, da dan wasan baya na Lille Jose Fonte.

Neymar

Ronaldo ya kasance dan wasa na baya-bayan nan da ya kamu da cutar coronavirus a daidai sa’adda zagayen na biyu na annobar COVID-19 ya fara kankama, bayan da aka bayyana cewa wasu shahararrun ‘yan wasa irin su Neymar, Kylian Mbappe da Zlatan Ibrahimovic duk sun kamu da cutar.

Kyliam Mbappe

A makon da ya gabata ma an tabbatar da kamuwar ‘yan wasa 5 a kungiyar kwallon kafar Eagles ta kasar Mali, da suka hada da Molla Wague, Boubakar Kouyate, Ali Yirango da Hamidou Traore.

Hukumar kwallon kasar Mali ta ce an kuma gano wasu biyu da suka kamu da cutar, amma ba ta bayyana sunayensu ba, kuma akan haka ne aka jingine fafata wasan da kasar ta shirya bugawa da Iran a ranar Talata.

Your browser doesn’t support HTML5

Kudi Bai Kare Shi Daga COVID-19 Ba: Cristiano Ronaldo Ya Kamu Da Cutar Corona