Adamawa:Ruftawar Gada Ta Hana Zirga-Zirga Tsakanin Michika Da Madagali

Motocin sufuri

Yanzu haka ba shiga ba fita a yankin Michika da Madagalin na jihar Adamawa a sakamakon rugujewar babban gadar da ta hada yankin da sauran sassan jihar.

Kamar yadda rahotanni ke nunawa , yanzu haka ba shiga ba fita a yankin Michika da Madagalin na jihar Adamawa a sakamakon rugujewar babban gadar da ta hada yankin da sauran sassan jihar. Wannan al’amari yanzu haka ya jefa al’ummomin da suka koma muhallansu bayan da rikicin Boko Haram ya tashe su cikin halin zulumi da rashin sanin tabbas.

Idan ma ba’a mance ba, ko a baya gadoji da dama ne yan bindiga masu tada kayar baya na Boko Haram suka dasa musu bama-bamai wanda kawo yanzu ba’a gyara su ba, kuma ana cikin wannan hali, sai kuma ga shi ruwan saman da aka yi kamar da bakin kwarya ya rushe gadar da ake dan lallabawa ana ketarawa, gadan Dilichim dake kusa da Bazza.

Yanzu haka matafiya da dama ne da suka hada da kungiyoyin bada tallafi da ke son zuwa yankin lamarin ya shafa, kamar yadda shugaban karamar hukumar Madagali Yusuf Muhammad wanda lamarin ya rutsa da shi a yau, yake kokawa.

Baya ga wannan babban gada na Dilichim, haka nan akwai wasu gadoji da suma suka rushe kamar yadda mataimakin shugaban karamar hukumar Michika Alh. Aliyu A. Kwaji ya shaida wa wakilin sashen Hausa Ibrahim Abdulaziz ta wayar tarho.

‘Yan majalisar dokokin jahar sun dade suna gabatar da kudurin neman a gaggauta gyara gadojin da aka lalatan, to amma ya zuwa yanzu shiru kake ji. Mr Adamu Kamale shine yake wakiltar mazabar Michika da Madagali yace sun yi mamaki da har yanzu babu wani abu da aka yi.

Your browser doesn’t support HTML5

Ruftawar Gada Ta Katse Michiga Da Madagali Da Sauran jahar Adamawa