Rundunar Gamayyar G5 Ta Sahel Na Fama Da Karancin Kayan Aiki

  • Ibrahim Garba

Wasu sojojin G5 da kayan yakinsu

Yayin da yaki da ta'addanci ke dada zama da sarkakkiya, rundunar gamayyar G5 mai yaki da Boko Haram da sauran kungiyoyin mayaka a yankin Sahel na Afirka, ta fara kokawa da rashin kayan aiki.

Rundunar Gamayyar G5, wadda hadaka ce ta sojoji daga kasashe biyar na yankin Sahel, wadda aka kafa ta don yakar 'yan bindiga irin su Boko Haram da al-Ka'ida, ta fara fama da rashin kudi da kuma rashin hadin kai tsakanin kasashen da su ka kafa ta, al'amarin da wasu jami'ai da kwararru ke fargabar ka iya gurgunta yakin da ta ke yi da ta'addanci.

"Abin da ya fi kawo damuwa game da makomar rundunar G5 ta Sahel, shi ne rashin wadataccen kudi da goyon baya daga manyan kasashen yankin," a cewar Seth Jones shugaban sashin nazarin barazanar da ke addabar kasashe, a cibiyar nazarin dabarun bullo ma al'amura da kuma kasa da kasa (CSIS, a takaice), wadda ke sa ido kan abubuwan da ke gudana a yankin, a hirarsa da Muryar Amurka.

"Babu wata daga cikin kasashe biyar na G5 da ke da wadataccen kudi ko kwarewa - kai ko da ma da hadin kan wata - da za ta iya abin da ya dace wajen gurgunta kungiyoyin ta'addanci a yankin," a cewar Jones.