Rundunar 'Yan Sandan Najeriya Ta Nemi Taimakon Sojojin Sama

Sufeto janar na ‘yan sandan Najeriya ya gana da babban hafsan sojin saman Najeriya don duba yadda zasu yi aiki tare wajen kawo karshen matsalar satar mutane.

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta nemi taimakon rundunar sojojin saman kasar wajen tunkarar masu satar mutane da ma ‘yan bindigar da a halin yanzu suke cin karen su babu babbaka.

Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu Abubakar, a lokacin da ya je helkwatar tsaron kasar inda ya gana da manyan kwamandojin sojojin saman kasar, ya nemi taimakon sojojin a fannin tattaro bayanan sirri na taswirar dazuzzukan hanyar Abuja zuwa Kaduna da kuma na yankin Birnin Gwari don kawo karshen Masu satar mutane.

Shugaban ‘yan sandan da ya fadi cewa lallai kam matsalar satar mutane a Najeriya yanzu na kara ta’azzara, abinda ke kara tsananta matsalar tsaron yankin Zamfara da kuma ke fantsamowa wuraren yankin Abuja.

Sufeto Mohammed Abubakar yace rundunar ‘yan sanda bata da karfi ta sama, dalilin da ya sa kenan ta ke neman tallafin mayakan saman.