Sabbin Alkaluman Wadanda Suka Kamu da COVID-19 a Najeriya

Jami'in asibiti

Adadin masu kamuwa da cutar COVID-19 a Najeriya na ci gaba da karuwa a cewar hukumar NCDC mai kula da dakile yaduwar cututtuka ta kasar.

Wannan bayanin da hukumar ta rubuta a shafinta na Twitter a ranar Juma’a 3 ga watan Yuli ya bayyana cewa mutum 454 suka kamu da cutar a ranar, yanzu gaba dayan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar ya kai 27,564 a kasar.

Jihohi 19 ne suka sanar da samun karin wadanda suka kamu da cutar, ciki har da Legas da ta samu mutum 87, 63 a Edo, 60 a birnin Tarayya Abuja, 41 a Ondo, 32 a Benue, 31 a Abia, 29 a Ogun, 19 a Oyo, 17 a Kaduna.

Sauran jihohin sun hada Delta inda aka samu mutum 16, 15 a Enugu, 14 a Borno, 9 a Plateau, 8 a Nasarawa, 5 a Kano, 4 a Bauchi, 2 a Gombe, sai kuma 1 a Katsina da Kogi.

NCDC ta kuma ce ya zuwa yanzu mutum 11,069 aka sallama daga asibiti bayan haka mutum 628 sun mutu sanadiyyar cutar.