Sabon Hafsan Sojin Somaliya Ya Tsallake Rijiya Da Baya

Sabon Hafsan sojin Somaliya, Janar Ahmed Muhammed Jimale Irfid, ya tsallake rijiya da baya a wani harin kunar bakin waken da ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 15 kusa da tawagarsa a Mogadishu, a cewar jami'an gwamnati.

Fashewar ta auku ne bayan da sabon Ministan Tsaro Abdurrashid Abdullahi Mohammed da kuma tsohon Hafsan soji Janar Mohammed Aden su ka bi ta hanyar, a cewar majiyoyin tsaro.

Sabon Hafan sojin na Somaliya na dawowa ne daga wata hidima a Ma'aikatar Tsaron kasar, inda ya maye gurbin Janar Aden.

An ce akasarin wadanda fashewar ta rutsa da su fararen hula ne da ke cikin wasu motocin bus-bus biyu.

Kungiyar mayaka ta al-Shabab ta yi ikirarin kai harin.