Shugaban Zimbabwe mai jiran gado Emmerson Mnangagwa ya dawo kasar jiya Laraba bayan ya shafe kimanin makwanni biyu ya na gudun hijira a kasar waje. Dawowar sa ya biyo bayan murabus din dadadden Shugaban kasa Robert Mugabe ranar Talata.
Kakakin Majalisar Dokokin Zimbabwe y ace za a rantsa da Mnangagwa a matsayin sabon shugaban kasa a gobe Jumma’a. Mnangagwa, wanda shi ne tsohon Mataimakin Shugaban kasar, ya gudu daga kasar, haka kwatsam bayan da Shugaba ya kore shi.
Wani babban jami’i a Cibiyar Hulda da Kasashen Waje na Amurka John Campbell, yace ganin yadda Mnangagwa ya taka muhimmiyar a gwamnatin Mugaba, bai tsammanin za a ga wani canjin kirki a salon gwamnati cikin wani kankanin lokaci.
Mugabe, dan shekaru 93 da haihuwa, ya shugabanci Zimbabwe tun daga lokacin da kasar ta zamu ‘yancin kai daga Burtaniya a 1980.