‘Yan kabilar Rohingya sama da rabin miliyan suka tsallaka iyaka zuwa kasar Bangladesh dake makwabtaka da Myanmar a ‘yan makonnin nan, mutanen dai na gujewa gallazawar da sojojin Burma ke yi, bayan da ‘yan tawayen Rohingya suka kaiwa jami’an tsaron kasar hari.
Fattakar da ake yiwa ‘yan Rohingya, wadda ta yi sanadiyar kisan kare ‘dangi, ta janyo suka da Allah wadai daga kasashen duniya, duk da yake har ya zuwa yanzu hukumomin Myanmar na ci gaba da musunta tashin hankalin da ke faruwa a kasar.
Jawabin sakatare Tillerson na zuwa ne bayan wani rahoton kungiyar kare ‘yancin bil Adama ta Amnesty International, wanda cikinsa take zargin jami’an tsaron Myanmar da cin zarafin ‘yan kabilar Rohingya.
Rahotan, wanda aka hada shi ta hanyar yiwa ‘yan gudun hira 100 tambayoyi, na cewa jami’an tsaron sun harbe daruruwan ‘yan Rohingya dake kokarin guduwa daga kauyukansu, suka kuma kone tsofaffi da marasa lafiyan da ba zasu iya guduwa ba.