Sakataren Harkokin Wajen Amurka Ya Kai Ziyara Nahiyar Asiya

John Kerry Sakataren Harkokin Amurka yayinda ya kai ziyara kasar Uzbekistan dake Asiya

Jiya Lahadi, sakataren harkokin wajen Amurka John kerry, ya gana da shugaban Uzbekistan dan kama karya da wasu jami'ai daga wasu kasashen dake Asiya ta tsakiya, wadanda ake zargin da zama wadanda suka fi ko wanne keta 'yancin Bil'Adama a fadin duniya.

Ziyarar da Mr Kerry ya kai Asiya ta tsakiya,tazo ne bayan rangadi da ya kai Turai da kuma Gabas ta Tsakiya. A jiya Lahadin ya gana da shugabannin kasashe biyar wadanda da suke karkashin ikon kasar Rasha da can wato, Kazakhstan,Kyrgyzstan,Tajikistan, Turkmenistan da kuma Usbekistan, kasashen da duka suke nuna damuwa kan sake farfadowar kungiyar Taliban a Afghanistan da kuma shigar 'ya'yan kasashen cikin kungiyar ISIS. Babban jami'in difilomasiyya na Amurkan yayi magana kan wadannan batutuwa a ganawar da suka yi a birnin Samarkand.

Jami'an Amurka suna kallon ziyarar da Mr. kerry ya kai a zaman matakin kara tabbatarwa kasashen da suke yankin Asiya karfin danganatakarsu da Washington, a dai dai lokacinda dangantaka tsakanin Amurka da Rasha take tabarbarewa. Haka nan ma akwai matsin lamba kan Mr.Kerry yayi magana kan rashin mutunta hakkin Bil'Adama da shugabannin suke aikatawa.