Sakataren tsaron Amurka yace gargadin da shugaba Karzai na Afghanistan yayi alama ce ta wahalun talakawan kasar

Sakataren Tsaron Amurka Robert Gates

Sakataren tsaron Amurka Robert Gates yace jan kunnen da shugaban Afghanistan Hamid Karzai yayiwa rundunar kawance alama ce ta wahalolin da farin hula suka dade suna fama da shi.

Sakataren tsaron Amurka Robert Gates yace Amurka ta fahimci cewa jan kunnen da shugaban Afghanistan Hamid Karzai yayi wa rundunar kawancen kasa-da-kasa gameda kai hare-hare akan fararen hula, wata alama ce dake nuna wahalolin da mutanen Afghanistan suka share shekaru 30 suna fama da su. Mr.Gates yace yana da muhimmanci sassan biyu su bincike asaran rayukkan da aka yi na fararen hula, kuma yana da kyau Mr. Karzai ya fahimci cewa kasarshi da NATO kawayen juna ne. A jiya Talata ne dai shugaba Karzai ya ja kunnen NATO akan cewa kada ta dauki kanta a matsayin “rundunar mamaye” kasar Afghanistan. Jan kunnen ya biyo ne bayan mutuwar mutane fararen hula da dama a sanadin hare-haren jiragen saman NATO.