Sane Ya Koma Bayern Munich

  • Murtala Sanyinna

Leroy Sane

Kungiyar kwallon kafar Bayern Munich ta kasar Jamus ta tabbatar da sayen dan wasan Manchester City ta Ingila Leroy Sane a kwantaragin shekara biyar, akan kudi akalla yuro miliyan 50.

Duk da yake har yanzu Bayern din bata kai ga biyan kudin ba, amma kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa ta amince ta biya kudi yuro miliyan 54.8 na sayen dan wasan.

Sane wanda ke da babban Muradin lashe gasar zakarun Turai, ya ce “Bayern babbar kungiya ce da ke da babban buri. Alkiblarsu kuma ta yi daidai da tawa manufar.”

Dan wasan dan kasar Jamus, na fatan hadewa da kocin Bayern din Hansi Flick, wanda ya jagoranci kungiyar ta lashe gasar Bundesliga karo na 8 a jere, a farkon sherarsa a kungiyar.

“Na san Hansi tun daga kungiyar ‘yan wasan kasar Jamus ‘yan kasa da shekaru 21, mun yi kyakkyawar dangantaka da shi a lokacin” in ji Sane.

Shugaban kungiyar Karl-Heinz Rummenigge, ya bayyana matukar farin cikin samun dan wasan. Ya ce “kwararren dan wasa ne da ya nuna kwarewarsa tsawon shekaru, musamman gudummuwar da ya ke bai wa kungiyar kwallon kafar kasarsa.”

Sane ya lashe gasar Premier har sau 2 tare da kungiyar Manchester City, inda ya zura mata kwallaye 39 a cikin wasanni 135, tun sa’adda ya koma kungiyar a shekarar 2016.