Sarkin Gombe Ya Rasu

Bayan share lokaci yana jinya, Alhaji Usman Shehu Abubakar ya rasu.
Barden Gombe Alhaji Amadu Jibrin shine ya bayyana cewa sarkin ya rasu ne da misalin karfe biyu na rana a kasar Ingila a lokacin daya tafi yin jinya.

Haka ma Gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Ibrahim Hassan Dankwambo ya bayyana rasuwar sarkin ta bakin Sakataren gwamnatinsa, Alhaji Sulei Bage.

Kafin rasuwarsa, Alhaji Usman Shehu Abubakar shine shugaban kungiyar masarautun Gombe.

Masarautar Gombe tace za'a dawo da gawar Alhaji Usman Gombe, inda za'a birne shi.