Saudiya Ta Mika Zainab Ga Ofishin Jakadancin Najeriya

Zainab H. Aliyu

Rahotanni daga Najeriya na cewa an saki matashiyar nan ‘yar Najeriya mai suna Zainab Aliyu, wacce hukumomin Saudiyya suka tsare ta bisa zargin safarar miyagun kwayoyi.

An sake ta ne bayan da hukumomin Najeriya suka shiga tsakani, bayan kuma da aka gano cewa ba ta da laifi kan abin da ake tuhumatar ta da shi.

“Yanzun nan muka yi magana da ita, an sake ta, ta na hannun hukumomin ofishin jakadancin Najeriya.” Inji mahaifin Zainab, Habibu Nuhu Kila, yayin wata hira da ya da Muryar Amurka ta wayar talho.

A cewar mahaifin na ta, shi ya fara gabatar da korafi ga hukumar da ke yaki da masu sha da safarar miyagun kwayoyi ta NDLEA da ke filin tashin jirage na Malam Aminu Kano bayan da aka kama ‘yarsa watanni hudu da suka gabata.

An dai kama Zainab ne, bayan da wani gungun mutane da suka shahara wajen safarar kwayoyi ya saka mata kwayar Taramadol a cikin Jakarta.

“Wadannan da suka aikata laifin na gansu, kuma sun fada, kuma an gani a wayoyinsu yadda suka yi magana, duk akwai abin da suka fada kan wannan batu.” Inji Nuhu.

Tuni ita ma’aikatar shari’ar Najeriya, ta tabbatar da cewa hukumomin na Saudiyya sun saki Zainab.

“Yanzu haka maganar da ake yi, an mika ta ga ofishin jakadancin Najeriya da ke Saudi Arabiya, kuma ma’aikatan sun riga sun karbe ta.” Inji Ministan Shari’a, Abubakar Malami, yayin wata hira da Muryar Amura ta wayar talho.

Ya kara da cewa, “maganar dawowar Zainab gida (Najeriya), batu ne da ke da wasu matsaloli na daban, wadanda ke da nasaba da harkoki da suka danganci tafiye-tafiye.”

Saurari cikakkiyar hirar Mahmud Lalo da mahaifin Zainab, Habibu Nuhu Kila:

Your browser doesn’t support HTML5

Saudiya Ta Mika Zainab Ga Ofishin Jakadancin Najeriya - 2'37"