Saudiyya Ta Kaurace wa Taron Malaysia

Taron Malaysia

Kasar Saudiyya, ta kasance daya daga cikin wasu kasashen da suka kaurace wa wani taron kwanaki hudu da aka shirya za a yi a Kuala Lumpur, domin duba kalubalen da duniyar Musulunci ke fuskanta.

Firai Ministan Malaysia, Mahatir Mohamad ne ya shirya taron, inda ake so a tattauna kan batutuwa kamar na halin da Musulmin Uighur ke ciki a Lardin Xinjian da ke China.

Taron Malaysia

Ana zargin hukumomin China da tsare miliyoyin ‘yan kabilar ta Uighur wadanda Musulmi ne, a wasu sansanoni ba da son ransu ba, zargin da Chinan ke musantawa.

Ita dai Saudiyya ta kaurace wa zaman ne saboda a cewarta, taron na gudana ne, ba tare da yawun kungiyar kasashen Musulumi ta OIC ba, wacce ke da hedkwata a Jedda.

A jiya Laraba kungiyar ta OIC, ta fitar da wata sanarwa, inda ta ce, irin wadannan taruka na kassara ayyukanta da na Musulunci.

Taron Malaysia

An dai tsara Firai Ministan Pakisatan, Imran Khan zai halarci taron, amma ya janye bayan da Saudiyya ta tursasa shi da kada ya je, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Sai dai kasashe irinsu Iran, Turkiyya, Qatar, wadanda ba sa dasawa da Saudiyya, na halartar wannan taro.