Saudiyya Ta Tsare Mutane 208 Bisa Zargin Cin Hanci da Rashawa

Mohammed bin Salman dan sarki mai jiran gado wanda yake aiwatar da yaki da cin hanci da rashawa

Ministan shari'ar kasar Saudiyya ya tabbatar da tsare mutane 208 da ake zargi da cin hanci da rashawa tare da wawure dukiyar jama'a da suka kai adadin dalar Amurka biliyan dari

Babban Atoni Janar din kasar Saudiyya, ya tabbatar da tsare wasu mutane 208, a wani wagegen binciken badakalar cin hanci da rashawa da ake yi, wanda aka yi kiyasin an salwantar da sama da dala biliyan 100 cikin shekaru da dama.

A wata sanarwa da ya fitar a jiya Alhamis, Saud al Mojeb, ya ce an saki mutane bakwai daga cikin wadanda ake tsare da su, yayin da 201 ke ci gaba zama a hannun hukuma.

Sannan ya ce gwamnati ta rufe asusun adana kudade kusan dubu-daya-da-dari-bakwai da ke bankuna.

Masu sukar gwamnatin Saudiyya, sun ce wannan bincike, wani yunkuri ne na yin waje-road da manyan jami’an gwamnatin kasar da kuma kare ‘yan adawa daga shiga harkokin gwamnati domin a dama da su, yayin da Yarima Mohammad Bin Salman mai shekaru 32 yake jagorantar sabuwar hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa da aka kafa.