Shawarar Da Buhari Ya Ba ‘Yan Najeriya Kan Coronavirus

Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su kwantar da hankalinsu dangane da yadda cutar coronavirus ke bazuwa a kasashen duniya.

A makon da ya gabata hukumomi a jihar Legas da ke kudancin kasar suka bayyana samun wani dan kasar Italiya dauke da cutar, wacce yanzu ake wa lakabi da COVID-19.

Mutumin, wanda ba a bayyana sunansa ba, ya koma Najeriyar ne bayan wani balaguro da ya yi zuwa birnin Milan.

Yanzu haka yana kebe a wani asibiti a jihar ta Legas.

“Shugaba Buhari yana kira ga ‘yan Najeriya da kada su razana da labarin bullar cutar ta COVID-19 wacce aka samu a karon farko a kasarmu,” kamar yadda wata sanarwa da kakakin shugaban Garba Shehu ya fitar da yammacin Lahadi.

Sanarwar ta kara da cewa, “nuna damuwa, ba za ta kara mana komai ba face kara haifar da wata illar.”

“A maimakon haka, ina kira ga ‘yan Najeriya da su bi shawarwarin da ma’aikatar lafiya da hukumar da ke yaki da yaduwar cutuka da kuma Hukumar Lafiya ta Duniya WHO suke bayar wa kan yadda za a kauce wa kamuwa da cutar.”

Buhari ya kuma yaba wa ma’aikatar lafiyar kasar dangane da irin matakan gaggawa da ta dauka domin “ganawo, tantacewa da kuma kebe” mutumin da aka fara samu da cutar.

Baya ga Najeriya wacce ta fi kowace kasa yawan jama’a a nahiyar Afirka, an samu bullar cutar a Algeria da kuma Masar.