Shawarar Trump Cewa Amurak Ta Hana Musulmai Shiga Kasar Ta Zama Masa Alakakai

Donald Trump dan takarar shugaban kasar Amurka a karkashin jam'iyyar Republican wanda yake son a hana musulmai shiga Amurka

Jiya Laraba, sukar da ake yiwa Donald Trump saboda shawarar da ya bayar na ganin Washington ta hana Musulmi shiga kasar na wucin gadi, sai karuwa suke yi

'Yan kasar Brutaniya kusan dubu metan ((250,000) sun sanya hanu kan takardar koke a internet, suna neman gwamnatin Ingila ta hana hamshakin dan kasuwar na gidaje shiga Brutaniya.

Wasu 'yan kasar Ingilan sun ce kalaman Trump, tamkar "kiyayya ce" daga nan suka yi kira ga gwamnatin kasar ta hana Trump shiga Ingila.

A Ingila duk takardar koke wacce ta sami goyon bayan mutane sama da dubu dari, ana muhawara kan batun a majalisar dokoki. Amma ministan kudi na Ingila George Osborne, ya gayawa wakilan majalisa cewa ba dai dai bane a hana " 'dan takarar shugaban kasar. "

A baya, Brutaniya ta hana mutane kamar su dan damben nan Mike Tyson,mawakain nan d a ake kira Tyler, malaman addinin Islama masu zazzafar ra'ayi, harda wani mai tsaurin ra'ayin addinin kirista Fred Phelps Sr.

A kasar Isra'ila 'yan siyasa daga masu ra'ayin rikau da masu ra'ayin gurguzu, da 'yan majalisa Larabawa duk sunyi Allah wadai da kalaman Mr. Trump suka ma bukaci a hana shiga kasar.

Amma waji jami'in gwamnatin kasar ya tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, Firayim Minista Benjamin Netanyahu, zai gana da dan kasuwar Donald Trump rana r 28 ga watan nan.

Akalla 'yan majalisar dokokin kasar daga bangaren 'yan hamayya sun rubuatwa Mr. Netanyahu wasika suka nemi da ya soke ganawarsa da Mr. Trump har sai ya janye furucin da yayi.