Shin Siyasar Najeriya Ta Raba Kan Kannywood Kenan Har Abada?

Aminu Sherif Momo, daya daga cikin fitattun jaruman Kannywood a Najeriya

Yayin da aka tunkari babban zabe a Najeriya, ya zuwa yanzu, zai yi wuya a bayyana adadin jarumai mata da maza na dandalin Kannywood da mawakan Hausa da suka shiga gangamin yakin neman zabe, domin tallata ‘yan takarar da suke marawa baya.

An ga fitattun jarumai irinsu Ali Nuhu, Adam A. Zango da mawaka irinsu Ado Gwanja da Rarara da dai sauransu, suna nuna goyon bayansu ga 'yan takarar da suka fi kwanta masu a rai musamman a matakin 'yan takarar shugaban kasa.

Akan ga fitattun mutanen, suna zuwa gangamin yakin neman zaben 'yan takarar tare da rera masu kayatattun wakoki, lamarin da masu lura da al'amura ke ganin ya haifar da rarrabuwar kawuna a tsakanin 'yan wasan kwaikwayon.

Sai dai jarumai irinsu Sani Danji da Al Amin, na ganin ba haka lamarin yake ba, domin kansu a hade yake kuma "da za ran an kammala siyasa za su koma ayyukansu," tare a cewar Al Amin.

Shin ko wanne irin tasiri wannan salon yakin neman zabe zai yi a fagen siyasar Najeriyar, musamman ma a arewacin kasar, lura da yadda jaruman mata da maza suka tsunduma tsundum wajen tallata 'yan takararsu.

Saurari cikakken rahoton Isah Lawal Ikara daga Kaduna:

Your browser doesn’t support HTML5

Shin Siyasar Najeriya Ta Raba Kan Kannywood Kenan Har Abada? - 2'29"