Cece-kuce Kan Shirin Bai Wa Jami'an Kiyaye Hadurra Makamai a Najeriya

Wasu jami'an hukumar kiyaye hadurra ta Road Safety a lokacin da suke taimakawa wajen kashe gobara

“Gwamnatin tarayya ta amince mana, kuma tuni jami’anmu sun yi horo kan yadda za su rika sarrafa makaman, na samu dammar kasancewa daya daga cikin wadanda suka gudanar da wannan horo shekaru biyu da suka gabata.” In ji Sini Kwabe, babban jami’i a hukumar ta FRSC.

A Najeriya, jama’a na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu, tun bayan da hukumar da ke kiyayen ukuwar hadurra, ta bayyana cewa, gwamnati ta amince, jami’anta su fara daukan makamai na bindiga.

Hukumar wacce aka fi sanin da Road Safety, ta ce ta mika bukatar neman a bai wa jami’anta makamai ne bayan da ta lura cewa ana samun karuwar aikata laifuka akan hanyoyi, a wasu lokuta ma har da kai hare-hare akan jami’anta.

“Gwamnatin tarayya ta amince mana, kuma tuni jami’anmu sun yi horo kan yadda za su rika sarrafa makaman, na samu dammar kasancewa daya daga cikin wadanda suka gudanar da wannan horo shekaru biyu da suka gabata.” In ji Sini Kwabe, babban jami’i a hukumar ta FRSC yayin wata hira da ya yi wakilin Sashen Ingilishi na Muryar Amurka, Timothy Obiezu.

Sai dai yayin da wasu ‘yan Najeriyar ke sambarka da wannan mataki, wasu kuwa akasin hakan suke nunawa.

“Bai wa jami’an na hukumar kiyaye hadurra makamai ganganci ne, saboda ni ban ga dalili ba, a da ai ba sa rike bindiga, kuma suna ayyukansu, da zaran ka ba su bindiga, babu wanda ya isa ya ja da su, kana tankawa za su harbe ka,” a cewar Moses Ndawo wanda direban tasi ne.

Amma a ganin masana a fannin tsaro irinsu Capt. Abdullahi Adamu Bakoji, lokaci ya yi da za a ba jami’an na Road Safety makamai.

“Ba za ka iya kare wani ba, ba tare da ka kare kanka ba, saboda suna kare lafiyar mutane ne su ma da lafiyarsu.” In ji Capt. Bakoji.

Ya kara da cewa, “saboda wani zai ga cewa ai wannan ma ba shi da bindiga, sai ka ga ya hau shi da fada da zagi wani lokaci har ma da duka.”

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, babu dai takamaiman lokacin da aka tsara da jami’an na hukumar ta kiyaye aukuwar hadurra za su fara amfani da makaman, amma dai ‘yan Najeriya sun zira ido su ga yadda lamarin zai kaya.