Shugaba Buhari Ya Mayar da Hankali da Munafukai -Gamawa

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Biyo bayan furucin Aisha Alhassan Ministar harkokin mata cewa tana goyon bayan ubangidanta Atiku Abubakar idan ya fito takarar shugaban kasa a shekarar 2019, har yanzu ana kai ruwa rana yayinda wani dan jam'iyyar APC ya kira shugaban kasa ya yi hankali da munafukai

Yanzu haka dai yan kasar na cigaba da tsokaci da kuma mayar da martani game da kalaman da ministan harkokin mata Sanata Aisha Jummai Alhassan tayi na cewa.

A'isha Jummai Alhassan Taraba ministar harkokin mata

Ministar tace ba za ta zama butulu ba wajen bijirewa ubangidan siyasarta kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar. Furucinta ya sa ma ministan wasanni Solomon Dalung kira ga shugaba Buhari da ya sauketa daga mukaminta.

To sai dai kuma yayin da wasu ke sukan kalaman Aisha Jummai Alhassan,wasu masana siyasa na ganin ministar ta yi daidai tunda bata butulcewa ubangidanta na siyasa ba.

Muhammadu Iliyasu Gamawa wani dan jam’iyar APC da ya san babbaku da farfarun siyasar kasar,yace bai kamata ma shugaban kasa ya damu da irin wannan cece-kucen ba.

Ba tun yau ba ne ma dai ake kai ruwa rana a tsakanin ministar da wasu yan siyasar jihar Taraba, jiharta ta asali,wadanda Aisha Jummai tace suke yada wannan yamidi din.

Koma da menene dai yanzu lokaci ne kawai ke iya tabbatar da ko shin shugaba Buhari zai yi garambawul ga majalisar Ministocin ko kuma a’a?

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Shugaba Buhari Ya Mayar da Hankali da Munafukai -Gamawa -3' 14"