Shugaba Jonathan Ya Mayar Da Martani Kan Wasikar Obasanjo

Shugaba Goodluck Jonathan

Watanni uku bayan da tsohon shugaban Najeriya Obasanjo ya rubutawa shugaban Najeriya Jonathan wasika mai shafi 18, yanzu shugaban ya mayar da martani.
Kimanin makwanni uku ke nan da tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya rubutawa shugaban kasar na yanzu Goodluck Jonathan wata wasika mai shafi 18 da ta kunshi batutuwa masu mahimmanci da yawa har ta tada kura mai ban tsoro a kasar.

Yanzu dai shugaba Jonathan ya mayar da martani kan wasikar da tsohon shugaban kasar Obasanjo ya rubuta masa.Martanin na shugaba Jonathan ya zo ne makwanni uku bayan wasikar da tsohon shugaba Obasanjo ya rubuta masa ranar 2 ga wannan watan. Shugaba Jonathan ya bayar da dalilai goma na mayar da martanin.

Ya yi la'akari da matsayin tsohon shugaba Obasanjo wanda ya yi shugabancin kasar na soji da na farar hula lokacin dimokradiya.Ya kuma yi la'akari da irin abun da ka biyo bayan wasikar ta Obasanjo. Jonathan wanda ya ce yana iyakacin kokarinsa na tabbatar da tsaro ya ce matsalolin ma ai gadonsu ya yi daga gwamnatocin da suka shude har da na Obasanjo.Misali, fashi da makami ya samo asli ne tun yakin basasan kasar.

Abun da ya fi damun Jonathan shi ne lissafa wasu jerin mutane 1000 da Obasanjo ya ce shugaban na shirin kashewa ta hanyar horas da wasu gwanayen maharbi daga nesa. Jonathan ya ce a matsayin Obasanjo na krista kuma ya ambaci sunan Allah har sau 17 a wasikar to ya rataye littafin Bible a wuyansa ya rantse cewa ikirarin da ya yi gaskiya ne.

Da ma batun shirin kashe mutane da aka ce za'a yi amfani da Manjo Al-Mustapha ya sa wata kungiya mai suna Great Najeriya ya yi taro tana wanke Al-Mustapha daga zargin. Abdulaziz Suleiman shi ne kakakin kungiyar ya ce idan tsoho bai ji kunyar hawan basukur a kasuwa ba, basukur din ma ba zai ji kunyar kayar da shi a kasuwa ba. Ya ce idan basu daina ire-iren wadannan zargi ba to zasu tona masu asiri domin suna da sunayensu kuma sun san laifukan da suka yi shi ya sa suna tsoron a saki Al-Mustapha. Sun umurci lauyoyinsu su shirya takardun kai kara a kasar da kotun bahasi na duniya domin a tabbatarwa Al-Mustapha hakinsa na dan adam.

Dan PDP kuma masanin tattalin arziki Aminu Danarewa Kurfi ya ce ina ma da Jonathan bai mayara da martanin ba. Ya ce ana batun kirsimati da karshen shekara yanzu kuma ga wata sabuwar wasika to da wanne ne za'a ji da shi? Yace kamar su 'yan boko dariya suke yiwa wasikun. Tambayoyin da Obasanjo ya yi akwai da yawa da ba'a bashi amsa ba ko kuma ba'a ba 'yan Najeriya amsa ba. Ya ce Obasanjo ya tsorata mutane ya ce akwai mutane 1000 kuma akwai 'yan arewa cikinsu da wai Jonathan na kokarin kashewa. Ya ce akwai lokacin da aka yi wata gwamnati da ta sa kowa tsoro ko dama gaskiya ka fada. Yau Allah ya kawo dimokradiya kuma a ce cikin dimokradiya baka iya fadin gaskiya. Ya ce muna cikin halin wani tsaka mai wuya.

Nasiru Adamu El-Hikaya nada karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Shugaba Jonathan ya Mayar da Martani Kan Wasikar Obasanjo - 3:03