Shugaba Obama Bai Yi Harsashen Satar Shiga Kwamfuta Zai Yi Tasiri A Zabe Ba

Shugaban Amurka mai barin gado Barack Obama

A yayinda hukumar leken asirin Amirka ta tantance cewa kasar Rasha tayi shishigi a zaben shugaban Amirka, shugaba Barack Obama yace yayi kuskuren hasashen irin tasirin da yakin neman zaben karya da satar shiga computa zai dora akan tsarin mulkin demokradiya.

Shugaban wanda saura kwanaki goma sha biyu, ya sauka daga kan ragamar mulki yayi wannan furucin ne a wani shirin gidan talibijin na ABC da ake cewa This Week.

Shugaba Obama yace bai yi kuskuren zaton shugaba Vladimir Putin na Rasha zai bada umarnin asawa tsarin demokradiya da zaben shugaban kasa kafar angulu ba.

To amma yace yana zaton yayi kuskuren cewa a wannan zamani akwai yiwuwar ayi satar shiga computa cikin tsarin dake baiyane.

Hukumar leken asirin Amirka ta hakikance akan cewa kasar Rasha ta kwarmata sakonnin e-mail na shugaban yakin neman zaben Hillary Clinton John Podesta.

Yawancin sakonnin sun baiyana dala dalan abun kunyar yadda yan jam’iyar Democrat suke kokarin ganin cewa Hillary Clinton ta doke abokin hamaiyarta Senata Bernie Sanders a zaben tsayar da dan takara.