Shugaba Obama Ya karbi Bakuncin Shugaban Gabon A Fadar White House.

Babban sakataren majalisar dinkin duniya Ban Ki-moon yake tattaunawa da shugaban Gabon,Ali Ben Bongo.

Alhamis ce shugaban Amurka Barack Obama ya karbi bakuncin shugaban Gabon Ali Ben Bongo a fadar White House, a tattaunawar da ake jin zai maida hankali kan harkokin tsaro a shiyyar Afirka.

Alhamis ce shugaban Amurka Barack Obama ya karbi bakuncin shugaban Gabon Ali Ben Bongo a fadar White House, a tattaunawar da ake jin zai maida hankali kan harkokin tsaro a shiyyar Afirka.

Jiya Laraba fadar White House ta kare shawarar shugaba Obama na ganawa da shugaban na Gabon, mutuminda shi da iyalinsa suke shan zargi kan cin hanci da rashawa.

Kakakin fadar White House Jay Carney, yace Mr. Bongo yana kaddamar da sauye sauye, ya kara da cewa Gabon ta taimaka a kawancenta da Amurka kan rikici a Ivory Coast, Libya, da Iran.

Gabon ce take jagorancin kwamitin sulhu na majalisar Dinkin Duniya na karba karba cikin watan nan.

Jiya laraba ce Mr. Obama ya gana da shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a fadar White.

A wani mataki na ba safai ba, Fadar White House, bata bada bayanan ganawarsa shugaban na Najeriya ba, sai yau Alhamis. A sanarwar da fadar White House ta bayar yau kan ganawar, tace Mr. Obama yayi wa shugaba Jonathan barka, kan nasarar kaddamar da zabe cikin lumana fiyeda saura da akayi a ‘yan shekarun baya bayan nan.

Haka kuma shugaban Amurkan yayi kira ga Mr. Jonathan daya himmatu sosai kan yaki da cin hanci da rashawa.