Shugaba Trump Ya Ce Zai Haramta Tik Tok a Amurka

Manhajar Tik Tok

Shugaban Amurka Donald Trump ya je wasan golf a daya daga cikin filayen wasan da ya mallaka a jihar Virginia a ranar Asabar 1 ga watan Agusta bayan ya yi barazanar cewa zai haramta wata manhaja mallakar wani sanannen kamfanin China da ake amfani da ita a kafafen sada zumunci aiki.

Shugaban Amurka Donald Trump

“A game da Tik Tok, zamu haramta manhajar a Amurka, abinda Trump ya fada wa manema labaran da ke tare da shi kenan ranar Juma’a 31 ga watan Yuli a cikin jirgin Air Force One daga jihar Florida.

Shugaban ya ce ta yiwu zai yi amfani da dokar Shugaban kasa don haramta manhajar. Kafin shugaban ya bar fadar White House da safiyar Asabar zuwa wurin golf din a birnin Sterling da ke jihar Virginia, babu wani mataki da aka sanar.