Shugaba Trump Zai Yi Amfani Da Karfin Mulki

Yanzu haka lauyoyin gwamnatin Amurka sun himmatu sosai a kokarin da suke yi, na cika wa’adin umarnin kotu da ta bayar na zuwa yau juma’a da yamma, da su bada hujjojunsu na saka tambayar ko mutum dan kasa ne ko ba dan kasa ba, a cikin tambayoyin kidayar ‘yan-kasa da za’a yi a shekarar 2020, ko ta yanke cewar bata bukatar a saka tambayar da ka iya kawo rudani a cikin jerin tambayoyin da suke kunshe a takardar kidayar.

Wasu kotunan tarayya da kuma jihohi da suke kalubalantar matakin da gwamnatin Trump ta dauka na ta saka tambayar ko mutum dan kasa ne ko ba dan kasa ba, a kidayar jama’a suna neman kotu ta fayyace musu matakin.

Bayan da ma’aikatan shari’ar da na cinikayya na Amurka kawai suka ce sun janye abinda tun farko suka amince, ba zasu saka tambayar ko mutum dan kasa ba ne ko ba dan kasa ba a cikin takardun tambayoyin.

Sai dai kotun kolin Amurka tuni ta yanke hukunci cewa hujjojin da gwamnati ta bayar domin saka tambayar dan kasa ba su gamsar ba, na hakikanin bayanan dalilin abinda ya kamata a tambaya lokacin kidayar jama’a a Amurka da ake yi duk bayan shekaru goma.