Shugaban Amurka Na Farko Da Ya Shiga Korea Ta Arewa

Lokaci da shugaba Trump ya shiga yankin arewacin Korea

Ko da yake, babu wata alama da ta nuna cewa haduwar shugabannin biyu za ta zarce sama da ta daukan hoto kawai, amma mutane da dama suna fatan wannan gaisawa da suka yi za ta farfado da batun nukiliyan da ta wargaje a baya.

A yau Lahadi, Donald Trump ya zama shugaban Amurka na farko mai ci, da ya shiga kasar Korea ta Arewa, a lokacin da ya ziyarci yankin da ruwansa da dakaru, wanda ya raba tsakanin Korea ta arewa da ta kudu.

Shugaba Turmp ne ya gayyaci takwaran aikinsa Kim Jong Un, domin su yi wata ‘yar gajiyar ganawa a wannan yankin da ke kan iyakar kauyen da ake kira Panmunjom.

“Ina so na ce, wannan babbar karramawa ce a gare ni, wacce ban yi tsammani ba, kawai cewa na yi, ga ni na zo, ina so na yi magana da Shugaba Kim, sai ga shi mun hadu, har ma na tsallaka kan iyaka, wannan babbar karramawa ce a gare ni." Inji Trump.