Shugaban Kasar Senegal Ya Kai Ziyara Kasar Kamaru

Ziyarar Macky Sall Kasar Kamaru

Shugaban kasar Senegal Macky Sall ya kai ziyarar aiki kasar jamhuriyar Kamaru, domin yiwa takwaransa Paul Biya ta’aziyar hatsarin jirgin kasa da kuma karfafawa shugaban gwiwa a yakin da ake da Boko Haram.

Shugaba Macky Sall ya jinjinawa Paul Biya a kokarin da yake na yaki da kungiyar Boko Haram, a lokacin da yake yi masa maraba a fadar Yaoundé.

Shima babban bakon ya godewa shugaba Paul Biya da uwargidansa dama sauran mukarraban gwamnati ga karamcin da suka nuna masa dafatan wannan ziyara zata kara dankon zumunci tsakanin kasashen biyu.

Macky Sall yace ya kai ziyaran ne domin jinjinawa kasar Kamaru a habbasan da sukayi na murkushe ‘yan ta’addar Boko Haram a jahar Arewa mai Nisa, haka kuma ya mika ta’aziyyarsa ga ‘yan kasar Kamaru wanda suka rasa rayukansu da kuma wadanda suka jikkata a hatsarin jirgin kasan da akayi.

Domin karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Shugaban Kasar Senegal Ya Kai Ziyara Kasar Kamaru - 2'15"