Shugaban Koriya ta Arewa Ya Karbi Bakuncin Manyan Jami'an Koriya ta Kudu

Shugaban Koriya ta Arewa ya karbi bakuncin manyan jami'an Koriya ta Kudu a fadarsa

Har yanzu wasan Olympic da aka kammala a Koriya ta Kudu na ci gaba da yin tasiri tsakanin kasashen Koriya biyu da basa ko ga maciji da can kafin wasan amma sai gashi Koriya ta Arewa ta karbi bakuncin manyan jami'an gwamnatin Koriya ta Kudu

Jami’ai a Seoul sunce shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un ya karbi bakuncin manyan hadiman shugaban kasar Koriya ta Kudu Moon Jae-in a wata walimar cin abincin dare jiya Litinin, a wani yunkurin diplomasiya da ake gani zai iya share fagen tattaunawa tsakanin Amurka da Koriya ta Arewa.

Tawagar Koriya ta Kudu mai mutane goma karkashin jagorancin babban mai ba shugaba Moon shawarwari kan harkokin tsaro Chung Eui-Yong, ta isa Pyongyang ne bayan tafiyar kai tsaye ta jirgin sama daga Seoul, abinda ba kasafai aka saba gani ba.

Da aka tambaye ta game da ganawar tsakanin koriyawan, sai kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka mai kula da harkokin yankin Asiya da Pacific Katrina Adams ta bayyana cewa, Washington na tuntubar Seoul a kai a kai domin Magana da yawu daya da Koriya ta arewa, da ta hada da bukatar kara matsa lamba domin raba yankin Koriya da makamai.

Adams ta fada a wata sanarwa cewa, “ba zamu sake maimaita kurakuran da gwamnatocin da suka gabata suka tafka ba, a shirye muke mu tattauna da Koriya ta Arewa domin mu jaddada matsayinmu kan bukatar raba yankin Koriya da makaman nukiliya, da ba shi da makawa.