Shugaban Najeriya Ya Bayyana Juyayi Kan Kuskuren Sojin Sama A Borno

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Kuskuren da mayakan saman Najeriya inda suka jefa wa 'yan gudun hijira bamabamai da suka kyautata zaton 'yan Boko Haram ya haddasa hasarar rayuka da dama

Rahottani daga Nigeria sunce mutane fiyeda 50 suka rasa ransu a sanadin wani kuskuren da rundunar sojan sama ta kasar tayi, ta saki bama-bammai akan fararen hula dake cikin wani sansanin ‘yan gudun hijira, yayinda take farautan mayakan Boko Haram a jihar Borno.

Daga cikin wadanda abin ya shafa, ko bayan mazauna sansanin, harda ma’aikatan bada agaji na kungiyoyi irinsu Doctors Without Borders, Red Cross da sauransu.

Yayinda shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari ke bayyana juyayi kan wannan al’amnari, a can Bornon kanta, rundunar soja ta yiwa manema labarai magan gameda abin da ya faru: