Shugaban Nijar Ya Karrama Sojojin Kasar Domin Rawar da Suka Taka A Yaki da Boko Haram

Shugaban Nijar Issoufou Mahammadou

Shugaban Nijar ya jinjinawa sojojin hadin kwuiwa na kasashen yankin tafkin Chadi da suka yaki Boko Haram kana ya yaba da rawar da sojojin kasarsa suka taka a yakin.

Shugaba Issoufou Mahammadou ya bayyana gamsuwa da jaruntakar sojojin da suke wakiltar kasar Nijar a kawancen saboda haka yace sun cancanci ya sadakar masu da lambar yabo da aka bashi a karshen watan jiya.

Wannan yunkuri na shugaba Issoufou Muhammadou ya dadadawa wasu 'yan kasar Nijar rai saboda acewarsu hakan zai karawa askarawan kasar kuzari a wajen yakin dake bukatar dagewa ba sassauci kamar yadda shugaban wata kungiya Abdulkadir Muhammad yace. Yace malam bahaushe ke cewa tuwon girma miyarshi nama. Abun kirki ne shugaban yayi domin zai karawa jami'an karfin gwuiwa.

A nasa ganin mai sharhi akan alamuran yau da kullum Ibrahim Kantama yace sun ji dadi amma tunda a hukumance shi ne shugaban sojojin wata rana ya daddage ya je ya ga sojojin a filin daga. Ya kwana, ya kuma ini a wurin yana jinjina masu yana kara masu karfin gwuiwa.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Shugaban Nijar Ya Karrama Sojojin Kasar Domin Rawar da Suka Taka A Yaki da Boko Haram - 3' 23"