Shugaba Omar el-Bashir Na Sudan Na Murna Da Dakatar Da Bincikensa

  • Ibrahim Garba

Shugaba Omar el-Bashir na Sudan

Shugaban Sudan Omar el-Bashir ya ce dakatar da bincikensa da Kotun Duniya ta yi babbar nasara ce ga shi da mutanen Sudan

Shugaban Sudan Omar al-Bashir ya yi ikirarin samun nasara kan Kotun kasa da kasa ta manyan laifuka, bayan da mai gabatar da kara na kotun ya dakatar da binciken zargin aikata laifukan yaki a Darfur.

Da ya ke jawabi jiya Asabar a birnin Khartoum, Shugaba Bashir ya ce mutanen Sudan sun yi galaba kan Kotun Kasa da Kasar ta wajen kin su mika jami'an gwamnatin Sudan ga abin da ya kira "kotun 'yan mulkin mallaka."

Ya ce Kotun da kanta ta amsa cewa ta gaza a matakan da ta ke daukawa a kansa.

Babbar mai gabatar da kara ta Kotun Kasa da Kasar Fatou Bensouda ta fadi ranar Jumma'a cewa ba ta da wani zabin da ya wuce dakatar da aikin bincike, a zargin da ake ma Bashir don a karkatar da kayan aikin zuwa ga wasu batutuwan da ke bukatar matakan gaggawa.

A wani jawabin da ta yi ga Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya, Bensouda ta ce Kwamitin Sulhun bai dage sosai ba, wajen ganin an damke Shugaban Sudan.

Zarge-zargen sun samo asali ne daga fafatawar da gwamnatin Sudan ke yi da 'yan tawaye a Darfur, tun a 2003. Kotun ta duniya ta tuhumi Mr. Bashir kan batutuwa daidai har goma, na laifukan yaki, da laifin cin zarafin bil'adama da kuma kisan kiyashi, wadanda aka aikata kan farar hula a yankin.