Za A Yi Rigima!: Shugaban Yankin Kataloniya ya ce kasar Andalusiya (Spain) Ba Ta Da Ikon Tsige Shi

  • Ibrahim Garba

Shugaban yankin Kataloniya Carles Puigdemont da wasu magoya bayansa

An karce kasa tsakanin yankin Kataloniya da Andalusiya (Spain) game da batun ballewar Kataloniya. Yayin da gwamnatin Spain ke cewa ta tsige Shugaba Carles Puigdemont na yankin na kataloniya, shi kuwa cewa ya ke Majalisar yankin ce kadai ke da hurumin tsige shi.

Tsigaggen Shugaban yankin Kataloniya Carles Puigdemont, jiya Asabar ya sha alwashin cigaba da gwagwarmayar neman ‘yancin yankin, bayan da gwamnatin Andalusiya ko Spain ta umurce shi da ya amince da rusa gwamnatinsa da ta yi.

Yankin Kataloniya na kasar Spain, wanda ya kasance da dinbin ikon cin gashin kai, a yanzu ya koma karkashin ikon gwamnatin Spain mai mazauni a birnin Madrid.

Bayan sauke manyan jami’an ‘yansandan yankin na Kataloniya da kuma ga rusa Majalisar yankin, Firaministan Spain Mariano Rajoy ya yi kiran da a gudanar da zaben gaggawa a Kataloniya a ranar 12 ga watan Disamba.

A jawabinsa na martani, Puidemont y ace Majalisar Dokokin Yankin na Kataloniya ce kadai ke da hurumin rusa gwamnatin yankin.

Amurka ne goyan bayan kokarin gwamnatin Spain na kare ta daga wargajewa a yayin da kuma kasar Rash eke goyon bayan ‘yan tawayen.