Shugabanni Na Amfani Da Talauci Da Rashin Ilimi

irin matasan da jam'iyun siyasa ke yin amfani da su, su na aikata abubuwan assha

Inji Ishaya Bajama da yake bayani akan siyasar kaiwa juna hare-hare a Najeriya

Bayan harin da wasu da ba'a san ko su waye ba suka kaiwa ofishin yakin neman zaben dan takarar dan majalisar dattawa a karkashin tutar jam'iyar PDP a jahar Zamfara suka kona shi kurmus, Grace Alheri Abdu ta ta tattauna da Ishaya Bajama akan wannan al'amari mai ban tsoro.

Ishaya Bajama ya fara ne da bayyana abun dake kawo haka:

Your browser doesn’t support HTML5

Ishaya Bajama kan siyasar Najeriya.- 4':37"


Ishaya Bajama dan gwagwarmaya ne na kare hakkokin bil Adama, kuma dan rajin neman ci gaban kasa, har wa yau kuma mai sharhi da fashin bakin al'amuran yau da kullum a Najeriya.