Shugabannin EU Sun Ce Zasu Karawa Burtaniyya Lokaci Bisa Sharadi

Shugabannin kungiyar kasashen Turai ta EU sun ce hakurin su ya kusa karewa gameda sha’anin Burtaniyya da shirin ta na fita daga kungiyar ta EU da ake kira Brexit da turanci, inda yanzu saura makonni biyu kafin a cimma wa’adin ficewar kasar daga kungiyar ta EU.

Akan haka ne, shugabannin na EU suka ce a shirye suke su karawa Burtaniyya lokaci amma fa a bisa sharudda masu wahala.

Daya daga cikin sharuddan shine cewa watakila za’a nemi Ingila ta sake gudanarda wata sabuwar kuri’ar jin ra’ayin jama’a gameda zama ko ficewarta daga kungiyar EU.

A ranar 21 ga watan nan ne dai Firayin-ministar Burtaniyya, Theresa May zata nemi kasashen na Turai da su jinkirta ficewar kasarta daga EU har zuwa watan Yuni mai zuwa.