Shugabannin FIFA, CAF Sun Kai wa Buhari Ziyara

Buhari da Infantino rike da jesi mai lambar 10 da sunan Buhari (Facebook/Femi Adesina)

Infantino na ziyarar kwana shida ne a Najeriya inda yake halartar gasar kwallon kafa ta mata da uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta shirya a tsakanin kasashe shida wacce ke gudana a Legas.

Shugaban hukumar kwallo kafa ta duniya FIFA, Mr Gianni Infantino da shugaban hukumar kwallon kafa na nahiyar Afirka Dr. Patrice Motsepe sun kai wa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ziyara a fadarsa da ke Abuja.

Wata sanarwa da kakakin Buhari ya wallafa a shafinsa na Facebook ya nuna cewa a ranar Alhamis shugabannin biyu suka kai ziyarar girmamawa ga shugaban na Najeirya.

Buhari da Infantino rike da kyallen FIFA, shugaban CAF Motsepe farce a hannun hagu (Facebook/Femi Adesina)

Yayin ziyarar, Buhari, ya ayyana cewa gwamnatinsa ta himmatu wajen bunkasa harkar kwallon kafa ta ‘ya’ya mata, a wani mataki na ganin an kwadaitar da su wajen samun abin yi a rayuwa.

Infantino na ziyarar kwana shida ne a Najeriya inda yake halartar gasar kwallon kafa ta mata da uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta shirya a tsakanin kasashe shida wacce ke gudana a Legas a cewar Adesina.

Yayin ziyarar Infantino da Motsepe a Abuja (Facebook/Femi Adesina)

Shugaban na FIFA, ya nuna godiyarsa ga irin matakan da gwamnatin Najeriya ke dauka wajen bunksa harkar kwallon kafa, yana mai kira ga Buhari da ya taimaka wajen yada sakonnin amfani da wasan kwallon kafa a matsayin hanyar samun hadin kai.

Wasu hotunan da fadar shugaban kasar ta wallafa, sun nuna Infantino da Buhari sun rike rigar kwallo da aka rubuta sunan “Buhari” a baya wacce aka ba shugaban.

Kazalika shugabannin kwallon kafar, wadanda suka samu rakiyar ministan wasanni Sunday Dare, sun ba shugaban wani kyalle mai dauke da tambarin hukumar ta FIFA.