Shugabannin Kabilun Nigeria Sunyi Taro A jihar Niger Domin Samar Da Zaman Lafiya.

  • Ladan Ayawa

NIGER: Taro kan dokokin ma'adanai

Domin inganta zaman lafiya a jihar Niger kabilu daban-daban dake zaune cikin jihar sun gudanar da taron kara fahintar juna.

Wakilan kabilun Nigeria daban-daban suka sami halartar wannan taron da niyyar inganta zaman lafiya.

Wakilin gwamnan jihar Neja a waje taron ya shaidawa mahalarta taron cewa jihar ta kowa da kowa ce, ba wani bare.

Wasu daga cikin wadanda suka yi jawabi a wajen taron sun bayyana muhimmacin zaman tare.

Ga Mustafa Nasir Batsari da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Shugabannin Kabilun Nigeria Sunyi Taro A jihar Niger Domin Samar Da Zaman Lafiya. 2'55