Shugabannin Kungiyar Meyetti Allah A Kudu Maso Yammacin Nigeria Sunyi Taro A Akinyele

  • Ladan Ayawa

NIGER: Taron Fulani Makiyaya

Shugabannin kungiyar Meyetti ALLAH da sarakunan Fulani a jihohin kudu maso yammacin Nigeria sun gudanar da taro a garin Ibadan, domi inganta zaman lafiya tsakanin makiyaya da manoma.

An gudanar da wannan taron ne a kasuwar shanu ta Akinyele dake cikin jihar Oyo.

Taron ya sami halarcin shugabannin kungiyar Meyetti-Allah, da sarakunan Fulani na jihohin Oyo, Osun, Ondo, Ogun, Ekiti, Kwara da kuma Lagos.

Shugabannin suka ce dalilin gudanar da taron shine domin su fada wa juna gaskiyar al’amurra, musamman game da huldan su da manoma.

Shugaban kungiyar Meyetti Allah na jihar Oyo, Alhaji Yaku Bello shine ya jagoranci taron.

Your browser doesn’t support HTML5

Shugabannin Kungiyar Meyetti Allah A Kudu Maso Yammacin Nigeria Sunyi Taro A Akinyele2;53