Shugabannin Wasu kasashen Afirka, Ciki Harda Goodluck Jonathan Suna Taro Kan Kungiyar Boko Harama A Paris

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan da shugaban Faransa Francois Holande

Yau Asabar ake sa ran shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, tareda takwarorinsa a yankin, zasu hallara a birnin Paris domin su tattauna kan yadda zasu tunkari kungiyar Boko Haram, wacce ta sace ‘yan mata ‘yan makaranta su fiye da metan a jihar Barno dake arewa maso gabashin kasar suna garkuwa dasu.

Taron da za a gudanar kan harkokin tsaro, shugaban Faransa Francosi Holande mai masaukin baki, taron zai kuma hada harda shugabannin kasashen Benin, da kamaru, da Nijar da Cadi. Ana kuma sa ran wakilai daga Amurka da tarayyar tturai da Britaniya zasu halarci taron kolin.

Shugaban Amurka Barack Obama yayi magana da Mr. Hollande jiya jumma’a, cikin batutuwa da suka tattauna harda hali da ake ciki a Najeriya. Kasashen biyu suna daga cikin kasashen yammacin duniya da suke taimakawa najeriya ayunkurinda kasar take na kubutar da ‘yan matan.

A ranar 14 ga watan jiya ne kungiyar ta kama, ‘yan matan, al’amari da dukkan duniya ta nuna bacin ranta a kai, da kuma zargin da ake yiwa gwamnatin Najeriya da kasa daukar matakan kubutarda ‘yan matan.