Shuwagabanin Kwastan na Afirka ta Yamma Zasu Taimaka Wajen Yakan 'Yan Boko Haram

Shugabanin Hukumar Kwastan na Afirka ta Yamma na Taro a Abuja Domin Shirya Daftarin da Za'a yi Amfani Wajen Ta'addanci
Shuwagabanin hukumar kwastan na Afirka ta yamma na taro a Abuja, domin shirya daftarin da za'a yi amfani dashi wurin yaki da ta'addanci da sifirin muyagun kwayoyi da makamai tsakani kasa da kasa.

Taron na kwana biyu, da mai baiwa shugaban kasa shawara akan harkokin tsaro, Kanal Sabo Dasuki mai retaya, ya bude zai nemo hanyoyin da hukumomin na kwastan na Afirka ta yamma zasu tallafawa Najeriya wajen yaki da kungiyar Boko Haram.

Shugaban, kwastan na Najeriya Dr. Abdullahi Dokko Inde, wanda shine mai masaukin baki "yace kowa yasan yanda kasar mu take, mutumin Nijer baka banbantashi da mutumin Katsina, mutumin Cotonou baka banbanmtashi da mutumin Legas, mutumin Kamaru baka banbantashi da mutumin Calabar."

Ya kara da cewa gaiyato shuwagabanin kwastan na yammacin Afirka zai taimaka wajen yaki da yan Boko Haram.

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumomin Kwastan na Kasashen Yammacin Afirka na Shirya Kudurin Yakar Ta'adanci - 5'01"